<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>389</hymn_number>
<title>Bisharar Yesu LW389</title>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu ya kira almajiransa sha biyu.
 Lokacin da yake komawa sama
 Ya ce, &quot;Su tafi su yi bishara
 Har duniya duka ta sami ceto.&quot;
 KORUS
 Bishara Yesu
 Za mu yi, za mu yi
 Babu tsoro fargaba ba za mu yi ba.

[V2]
 2) Sai ku fara a cikin Urushalima,
 Har in aiko maku da mai taimako.
 Ruhu mai tsarkina za ya bida ku,
 Ga shi ina tare da ku a kulluyaumi.
 Korus

[V3]
 3) Sai ku fara daga Urushalima,
 Samariya har da Galili.
 Dukan ƙauyuka suna bukatar ceto.
 Sa'an nan har iyakar duniya.
 Korus

[V4]
 4) Ku ɗauki giciyen Yesu domin bishara,
 Gama duniya tana mutuwa.
 Idan mu kyale su za su hallaka,
 Alhakinsu yana rataye a wuyanmu.
 Korus

[V5]
 5) Wanda ya nace cikin aikin bishara.
 Za ya sami ladan aikinsa.
 Za ya sami rawani na rai,
 Za mu yi mulki tare da shi har abada.
 Korus</lyrics>
</song>